Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cadi Tana Yaki da Boko Haram a Najeriya


Sojojin Najeriya.

Rahotanni daga yankin sunce Cadi ta shiga kasar a zaman wani mataki na hadin guiwa domin yaki da kungiyar.

Daruruwan sojojin Chadi suka shiga yankin arewa maso gabashin Najeriya a wani shirin hadin gwiwa na kasashen yankin domin kawar da ta’adancin Boko Haram.

Shaidun gani da ido sun ce sojojin Chadin sun tsallka daga Kamaru suka shiga garin Gamboru dake cikin Najeriya.

Wasu sojojin Chadin kuma kusan su 300 sun ja daga a Bosso, garin dake kan iyaka tsakanin Najeria da Nijar.

Mai magana da yawun gwamnatin tarayyar Najeriya , Mike Omeri, ya gayawa Sashen Hausa na MA cewa Chadi tana aiki ne da yarjejeniyar da kasashen yankin suka cimma na yakar ‘yan ta’adan dake yankinsu.
Kasar Chadi tana cikin kasashe hudu da suka sha alwashin taimakawa da yakar kungiyar Boko Haram. Sauran kasashen su ne Kamaru, Nijar da Binin.

Kungiyar Boko Haram ta mamaye wasu kananan hukumomin jihar Borno kana suka kwace wani yankin tafkin Chadi na kasa da kasa watan jiya.

Tun farko ranar Litinin da yamma dakarun gwamnatin Najeriya suka ce sun sake kwato wasu garuruwa daga hannun ‘yan Boko Haram da suka hada da Gamboru, Mafa, Mallam Fatori, Abadan da Marte.

To saidai kamfanin labarum kasar Faransa yace wani jami’in sojan Chadi ya karyata ikirarin gwamnatin Najeriya ya kuma kara da cewa ‘yan Boko Haram suna rike da garin Gamboru wanda suka kewayeshi da mayakansu.

XS
SM
MD
LG