Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

CAR: Tsoffin Firayim Ministoci biyu ne zasu fafatawa a zaben zagaye na biyu


Zabe a Afirka ta Tsakiya

Tsoffin firayim ministoci biyu daga Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, za su fafata a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa,wanda aka shirya za a yi a ranar 31 ga wannan wata na Janairu.

Sakamkon zabe a matakin farko da aka fitar a jiya Alhamis ya nuna cewa dan takara Anicet Goerges Dologuel na ga ba da kashi 24 na kuri’un da aka kada, yayin da Faustine Archange Toudera, wanda shi ne na biyu ke da kashi 19 cikin dari.

Fiye dai da ‘yan takara 30 ne suka tsaya neman shuagbancin kasar a zaben da aka yi ranar 30 ga watan Disambar da ta gabata, inda hukumar zaben kasar ta ce akalla kashi 79 na masu kada kuri’a ne suka fita rumfunan zabe.

A farkon wannan mako, wasu daga cikin ‘yan takarar sun nemi da a dakatar da kidayar kuri’un, bayan da suka yi zargin an tafka magudi da kuma wasu kurakurai da aka samu wajen gudanar da zaben.

Sai dai hukumar zaben ta yi watsi da korafe-korafen nasu, wadanda suka ce ba su da tushe.

Kasar ta Jmahurniyar Tsakiyar Afrika na kokari ne ta kafa sabuwar gwamnati domin maye gurbin wacce aka kafa ta wucin gadi a shekarar 2014, wato shekara guda bayan da ‘yan tawaye suka hambarar da gwamnatin Francois Bozize.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG