Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Carrie Lam Ta Ce Ba Zata Sauka Daga Mulki Ba


Lam ta fadawa manema labarai a yau Talata cewa “koda wasa bata yi tunanin” sauka daga kujerarta ta mulki ba.

Shugabar Hong Kong Carrie Lam, wacce ke fama da matsalolin mulki, ta ce a yau Talata ba ta da niyyar sauka daga kan gadon mulkinta, don kawo karshen zanga-zangar adawa da ake yi wa gwamnatinta, wacce ta girgiza birnin tsawon watanni uku, kuma ta musanta rahotannin da ke cewa shugabannin China sun hana ta sauka daga mulkin, tana mai cewa tana son ta magance rikice-rikicen siyasa na birnin da kanta.

Lam tana mayar da martani ne wa rahoton kamfanin dillacin labarai na Reuters game da wani muryar wanda a ciki aka ji ta tana gayawa gungun shugabannin 'yan kasuwa a makon da ya gabata cewa itace ta janyo wannan "fitinar"dake faruwa a Hong Kong, tunda itace ta fito da dokar da ta haifar da zanga-zangar.

Duk da haka, Lam ta fadawa manema labarai a yau Talata cewa “koda wasa bata yi tunanin” sauka daga kujerarta ta mulki ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG