Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cece-Kuce Akan Matsayin Nijar a Zaben Najeriya


Ya yin da shirye-shiryen zabe ya kankama a Najeriya, masu sharshi a jamhuriyar Nijar sun fara bayyana matsayinsu a game faruwar wasu abubuwan da ke nuna alamun Nijar na goyon bayan daya daga cikin ‘yan takarar zaben shugaban kasa mai zuwa.

Mawakan troupe Albishir, na jamhuriyar Nijar sun rera wakar kamfai ga dan takarar jam’iyyar APC a zaben shugaban kasar da za a gudanar a karshen mako a Najeriya, lamarin da tuni ya haifar da mahawara a yanzu haka a bisa yadda mawakan ke kwatanta wakar a matasyin wata gudunmawa daga shugaban kasar Nijar.

Muryar Amurka ta yi kokarin tuntubar jami’an kasar Nijar, domin jin abin da zasu ce kan wannan Magana, amma hakka bata cimma ruwa ba.

Wannan cece-kuce na faruwa ne kwanaki kalilan bayan da aka hango gwamnan jihar Zinder da na Maradi rataye da tutar APC a wuya a ya yin gangamin jam’iyyar na Kano, abin da ya janyo suka daga jam’iyyar adawa ta PDP wacce ke ganin an yi katsalandan.

Tuni dai kungiyoyi masu zaman kansu suka fara jan hankulan ‘yan Nijar a duk inda suke su nisanci kansu daga dukkan wani yunkurin shiga harakokin zabubukan da za a gudanar a ranar Asabar din da ke tafe a Najeriya don kaucewa fadawa tarkon ‘yan siyasa.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

Facebook Forum

Zauren VOA Hausa #EndSARS

Zauren VOA Hausa #EndSARS Kashi na Biyu 03
please wait

No media source currently available

0:00 0:18:31 0:00
Karin bayani akan #ENDSARS: Zanga Zangar Kyamar Gallazawa Al’umma Da Yan Sanda Ke Yi

Rayuwar Birni

Hira da Yusuf, wani dan asalin Jamhuriyar Nijar da ya shekara a Abuja yana sana’r gyaran takalmi
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00
XS
SM
MD
LG