Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cece-Kuce Kan Batun Karbar Haraji Daga Ribar Google Da Twitter A Najeriya


Mataimakin Shugaban Najeriya Prof. Yemi Osinbajo (Instagram/ Prof. Osinbajo)
Mataimakin Shugaban Najeriya Prof. Yemi Osinbajo (Instagram/ Prof. Osinbajo)

‘Yan Najeriya sun yi ta bayyana mabanbantan ra’ayoyi game da maganar mataimakin shugaban kasar, Farfesa Yemi Osinbajo, da ya ce Najeriya za ta duba yiyuwar amfani da tanadin doka wajen fara karbar haraji daga ribar da manyan kamfanonin sadarwa ke samu ta hanyar huldar kasuwanci da yan kasar.

A martanin da suka mayar kan wani sako da Mohammed Jamal da aka fi sani da white Nigerian ya wallafa a kafar Tuwita, wasu ‘yan Najeriya sun bayyana cewa bai kamata gwamnatin kasar ta dauki irin wannan mataki ba duba da yadda wadannan kamfanonin sadarwa kamar su Tuwita, Google, Facebook da dai sauransu ba su da ofisoshi a Najeriya kamar yadda Emmanuel Jacobs da aka fi sani da @Cryptowellsjah a Tuwita ya bayyana.

Emmanuel Jacobs ya kara da cewa, idan gwamnatin Najeriya ta dauki irin wannan mataki, hakan na nufin cewa, kamafanonin sadarwar ko yan Najeriya masu fasahohi a dandali kamar su playstore, apple store da ba su da ofis-ofis a kasashen duniya ma su rika biyan haraji kenan.

A nasa ra’ayi, Adebiyi Olukayode ya wallafa a shafinsa na Tuwita cewa harajin da mataimakin shugaban Najeriya ke nufi a kan sana’o’in da kamfanoni kamar su Tuwita ke karbar haraji a kai a hannun ‘yan kasar ne, inda ya yi misali da yadda kamfanin Netflix ke biyan haraji ga gwamnatin kasar Canada alhali kamfanin bai da ofis a kasar.

Mataimakin Shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ne ya bayyana batun na fara karbar haraji daga kamafanonin sadarwar a yayin wata tattaunawa da ya yi da wakilan kungiyar akantocin Najeriya wacce shugabanta Adesina Adebayo ya jagoranta zuwa fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya Abuja kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Nakeriya wato NAN ya ruwaito.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun mataimakin shugaban kasar, Laolu Akande, ya fitar a ranar Lahadi inda ya ruwaito, Farfesa Yemi Osinbajo na cewa, dokar kudi ta shekarar 2019 ta ba gwamnati damar fadada hanyoyin samun kudin shiga amma dai gwamnatin tarayya kasar ba za ta kara haraji a yanzu ba, in ji shi.

Dokar kudi ta shekarar 2019 ta ba gwamnati damar karbar haraji a bangarori da suka hada da karbar harajin daga manyan kamfanonin sadarwa na duniya da suke da tarin abokan hulda a Najeriya, ko da kuwa basu da ofisoshi na dindindin a nan, kuma a halin yanzu ba sa biyan harajin.

Haka kuma, Laolu Akanda a madadin mataimakin shugaban Najeriya ya yi la’akari da sashe na hudu na dokar kudi ta shekarar 2019, da ta ba ministar kudi karkashin izinin shugaban kasa, damar tantance me ake nufi da samun abokan hulda da yawa ga kamfanonin da ba na Najeriya ba.

Najeriya dai ta fuskanci matsin tattalin arziki musamman a shekarun baya-bayan nan sakamakon tasirin annobar korona birus, wanda gwamnatin ta ce ba zai yiwu ta matsa wa ‘yan kasar da karbar haraji ba saboda mutane a fusace suke sakamakon yanayin matsi da su ke wiki na rayuwa musamman da hauhawar farashin kayayyaki.

XS
SM
MD
LG