Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Champions League: Su Waye Za Su Buga Wasan Karshe?


Kofin gasar UEFA a lokacin da Bayern Munich ta lashe kofin a bara

An fitar da sunayen kungiyoyi takwas, wadanda za su kara a zagayen farko da na biyu a wasannin quarter final a watan Afrilu.

Tun bayan da aka fitar da jerin sunayen kungiyoyin da za su kara a wasannin quarter-final da semi-final a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai ta UEFA​, aka tayar wa da masu sharhi da masoya kwallon kafa tsimi.

Jama’a dai na ta tsokaci kan yadda wadannan wasannin za su kaya wadanda za a yi su a watan Afrilu mai zuwa.

A ranar Juma’a aka fitar da sunayen kungiyoyi takwas, uku daga Premier League, biyu daga gasa Bundesliga​, daya daga gasar Faransa ta Ligue 1 sai daya daga gasar La Liga da FC Porto ta Portugal.

Karin bayani akan: UEFA​, Bundesliga​, Real Madrid, Liverpool, PSG, Manchester City​ da gasar Premier.

Ga yadda aka tsara karawar kungiyoyin a Quarter Final:

Manchester City vs Borussia Dortmund

FC Porto vs Chelsea

Bayern Munich vs Paris Saint-Germaine

Real Madrid vs Liverpool

Wannan hadi ya sa jaruman gasar Premier Manchester City za su yi gaba da gaba da Borussia Dortmund – daya daga cikin wasannin da ake ganin za a yi kare-jini-biri-jini.

Bayern wacce ke rike da kofin gasar, ita ta doke PSG da ci 1-0 Lisbon inda suka lashe kofin gasar na bara.

Wani wasa kuma da zai dau hankalin masoya kwallon kafa shi ne tsakanin Liverpool da Real Madrid wadanda rabon da su hadu a tun a shekarar 2018.

A ranar 29 ga watan Mayu za a buga wasan karshe a birnin Istanbul na kasar Turkiya.

AFCON 2021, Kelechi Iheanacho

"Ku doke daya daga cikin shahararrun koci a duniya", Kelechi Iheanacho, Najeriya bayan sun doke Masar
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:11 0:00
Karin bayani akan Wasanni

AFCON 2021, Ahmed MusaQueiroz ta Masar

Queiroz ta Masar, "Ba mu kasance cikin filin wasa ba a farkon rabin lokaci 'yayin da' Najeriya ta ci nasara''
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:52 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021, Super Eagles

Najeriya na atisaye gabanin wasanta na farko da Masar a rukunin D na gasar AFCON
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:54 0:00
Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG