Accessibility links

Chief Solomon Doshep Lar ya yi magana kan zaman lafiya a jihar Filato.

Lokacin rigingimun jihar Filato Chief Solomon Doshep Lar ya jagoranci wani kwamitin sulhu kan samun zaman lafiya a Filato.

Yayin da abokiyar aiki ta zanta da shi game da aikin da aka sa kwamitin ya yi bayani.Ya ce su goma sha biyar aka nada kana suka duba su ga abun da gwamnati ta tsara masu su yi. Ya ce an basu kwana goma sha hudu ne kajal su yi taron neman bakin zaren rikicin jihar ta Filato.

Yayin da yake kira ga jama'ar Filato ya ce an sansu da zaman lafiya da son jama'a shi yasa aka bata suna jiha mai kauna mai kuma son baki. Ya ce sabo da haka bai kamata jihar ta rabu da wannan kyakyawan sunan ba. Ya kira kowa da kowa a taimaka a tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Ga karin bayani.
LABARI: Wasu 'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane A Jihar Adamawa. www.voahausa.com
Wasu 'yan bindiga sun kai hari a wani kyauye cikin jihar Adamawa dake kusa da iyaka da jihar Borno. www.voahausa.com

Kwanana kwanan nan al'ummar Adamawa ke murnar samun zaman lafiya da fatan gwamnatin tarayya zata cire masu dokar ta bacin da ta kakaba mata sai gashi wasu 'yan bindiga sun kai hari a wani kauyen jihar dake kan iyaka da jihar Borno, jihar da 'yan Boko Haram suka sake tayar da karin baya cikin watanni biyun da suka gabata. www.voahausa.com
XS
SM
MD
LG