Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban PDP Na Farko Ya Rasu Yau A Amurka


NATO harbiy samolyotlari Litva osmonida

Shugaban PDP na farko kuma tsohon gwamnan jihar Filato ya rasu a nan Amurka yau.

Allah Ya yiwa tsohon shugaban PDP na farko kuma tsohon gwamnan farar hula na farko a jihar Filato rasuwa yau da safe a nan Amurka.

Chief Solomon Doshep Lar gwamnan farar hula na farko a jihar Filato kuma shugaban PDP na farko a duk fadin Najeriya ya rasu yau da safe misalin karfe uku agogon Washington DC ko kuma karfe takwas agogon Najeriya.

Kodayake Chief Solomon Lar ya rasu ne a nan Amurka amma abokin aiki Aliyu Mustapha sai da ya tuntubi gwamnatin jihar Filato daga nan Amurka domin tabbatar da gaskiyar lamarin. Kwamishanan yada labarai na jihar Filato Abraham Yiljap shi ya tabbatar da rasuwar Chief Solomon Lar wanda kuma shi ne walin Langtang.

A jawabinsa Abraham Yiljap ya fara da yiwa iyalan marigayin ta'aziya da jihar Filato da ma Najeriya gaba daya. Ya ce da aka fada wa gwamnan Filato na yanzu ya mika ta'aziyarsa ga iyalan ya kuma ce sauran shirye shirye sai yadda iyalan suka shirya da kuma kawowar gawar daga Amurka. Amma duk da shirin iyalan gwamnatin tarayya da ta Filato su ne zasu dauki nauyin jana'izar.

Game da ranar da za'a kawo gawar Mr. Abraham Yiljap ya ce ba zai iya fada takamaimai ba domin lokacin da ya tuntubi iyalan sun ce sai sun gana kana su tsayar da ranar daukar gawar da yin jana'iza.

Ga karin bayyani
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:31 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG