Accessibility links

China Na Dab Da Kammala Rigakafin Coronavirus


China na kokarin shiga gaba wajen samar da rigakafin cutar coronavirus, a yayin da take kokarin yin amfani da rigakafin a siyasance domin daukaka martabar ta da matsayinta a duniya.

A yayin da China ta ke ikirarin kai karshe a samar da rigakafin cutar coronavirus, Beijin ta soma yin alkawarin samar da rigakafin cigin gaggawa ga wasu kasashe na musamman.

Ana ganin wannan kokarin a zaman wata hanya da Beijin ke kokarin amfani da ita wajen daukaka matsayinta a duniya, bayan barkewar annobar da ta soma daga birnin Wuhan ta kuma yadu a sauran sassan duniya.

Kasashe da dama da ke yankin kudancin tekun China, na cikin yankunan da Beijin ta ke kokarin yada gangamin difilomasiyyarta na rigakafin.

A cikin watan Yuli, Ministan Lamurran Cikin Gida na China ya yi wa kasar Philippines alkawarin ba ta fifiko wajen samar da rigakafin. A watan Agusta kuma wani babban kamfanin hada magunguna na China ya rattaba hannun yarjejeniya da kamfanin hada magunguna mallakar gwamnatin kasar Indonesia mai suna PT Bio Farma, domin samar wa Jakarta rigakafin har miliyan 250 kowace shekara.

A farkon watan Satumba, wani dan majalisar dokokin China Yang Jeichi, ya ziyarci Myanmar, ya kuma yi alkawarin cewa Beijin za ta ba da kulawa sosai ga Yangon ida har ta sami rigakafin.

Facebook Forum

Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

An Kai Wa Ofisoshin Kungiyar Ba Da Agaji Hari A Arewa Maso Gabashin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG