Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Ta Dakatar Da BBC Daga Gudanar Da Ayyukanta a Kasarta


Hedikwatar yada labaran BBC
Hedikwatar yada labaran BBC

Hukumar dake sa ido kan kafafen labarai a China, ta ce ta dakatar da kafar labaran BBC daga gudanar da ayyukanta a kasar, saboda abin da ta kira “Saba ka’ida sosai game da batutuwan yadawa a labarai.”

Wannan shawarar na zuwa ne mako guda bayan da Hukumar dake sa ido kan kafafen yada labarai ta Burtaniya, mai suna the Office of Communications, ta soke lasisin Gidan Talabijin din China na kasa da kasa.

Hukumar ta ce jam’iyyar Kwaminisanci ta kasar China ce ke tafi da harkokin wannan kafar labaran, wanda hakan ya saba ma dokar Burtaniya wadda ta hana jam’iyyar siyasa yin iko da kafar labarai mai lasisi.

A ranar Alhamis, Hukumar Gidan Rediyo da Talabijin na China (NRTA) ta ce an samu BBC da laifin, abin da ta kira, “Saba ma ka’idojin da aka gindaya ma kafafen rediyo da talabijin” a rahotonnin kafar kan China, wanda hakan ke illa ga muradun China da kuma hadin kan kabilunta.”

XS
SM
MD
LG