Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan fafatikan nan na China, Liu Xiaobo, zai sami lambar yabo

Wani dan fafatikar tabbatar da dimokaradiyya kenan ke rike da hoton dan fafatikan China dinnan da aka daure, Liu Xiaobo ya na kokarin tsallake shingen da 'yan sanda su ka gindaya lokacin zanga-zanga a ofishin jakadancin China Hong Kong

Dan fafatikan nan na China, Liu Xiaobo, zai sami lambar yabo ta Nobel ta zaman a yau Jumma’a, to amman ba zai iya karban kyautar tasa ba.

Dan fafatikan nan na China, Liu Xiaobo, zai sami lambar yabo ta Nobel ta zaman a yau Jumma’a, to amman ba zai iya karban kyautar tasa ba.

Liu dai na zaman wakafi na tsawon shekaru 11 a China bisa laifin yin karan tsaye ga ikon gwamnati.

China dai ta yi ta kokarin shawo kan kasashen duniya su kaurace wa bikin nay au Jumma’a a Oslo, kasar Norway. Ya zuwa yanzu dai a kalla kasashe 18 sun ki karban goron gayyatar. To amman wajen kasashe 45 sun amince su halarci bikin.

Amurka ta fadi jiya Alhamis cewa Jakadanta a Norway, Barry White, zai hallara. Fadar White House ta sake jaddada kiraye-kirayen China ta saki Liu.

Manyan jami’an sashen ‘yancin dan adam a Majalisar Dinkin Duniya da wasu manyan kungiyoyin rajin kare ‘yancin dan adam ma na kiraye-kirayen a saki Liu.

To amman China ta fadi jiya Alhamis cewa ba za ta bayar da kai bori yah au ba dukko da matsin lambar kasa da kasa na ta sake shi.

Liu Xiabao ya shiga zanga-zangar nan ta dandalin Tiananmen Square ta 1989 a Beijing kuma ya na daya daga cikin fitattun ‘yan fafatika masu gwagwarmayar tabbatar da ‘yancin siyasa da kuma ‘yancin dan adam a China.

XS
SM
MD
LG