Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Netanyahu Ya ce ba za a Raba Birnin Kudus Gida Biyu ba


Firayim Ministan Isira'ila Benjamin Netanyahu a lokacin da ya ke magana da 'yan jarida a Tel Aviv.

Farayim Ministan Isira’ila ya yi watsi da batun raba birnin Kudus da sabuwar kasar Falasdinu idan an kafa.

Farayim Ministan Isira’ila ya yi watsi da batun raba birnin Kudus da sabuwar kasar Falasdinu idan an kafa.

Mr. Netanyahu ya fadi jiya Lahadi cewa raba birnin Kudus bai dace da manufofin gwamnatinsa ba.

Falasdinwa dai na fatan cewa Gabashin Birnin Kudus da akasarin mazauna wurin Larabawa ne, zai kasance hedikwatansu, a sa’ilinda kuma gwamnatin Isira’ila ke zakewa cewa daukacin birnin Kudus Hedikwatanta ne.

Furucin na Mr. Netanyahu ya zo ne ‘yan kwanaki bayan da Ministan Tsaron Isira’ila Ehud Barack ya bayar da shawarar a raba birnin na Kudus gida biyu, don a cimma maslahar zaman lafiya.

Shugabannin Falasdinwa sun bayyana bacin ransu da tantamarsu game da makomar tattaunawar zaman lafiyar, bayan da Gwamnatin Amurka a karkashin Obama ta watsar da batun shawo kan Isira’ila ta sake dakatar da gine-ginen matsugunan Yahudawa a Yamma da kogin Jordan da Falasdinwa ke cewa nasu ne.

Ran Jumma’a Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton ta ce daga yanzu Amurka ba za ta kara zama na-zaune game da tattaunawar zaman lafiyar Gabas ta Tsakiya ba, amaimakon haka za ta iza bangarorin biyu su tinkari muhimman batutuwan ba tare da jinkiri ba.

A tashin hankalin jiya Lahadi, hukumar sojin Isira’ila ta ce dakarunta sun kashe Falasdinawa biyu da su ka yi kokarin kutsawa cikin Isira’ila daga Gaza. Isira’ila ta ce an hango mutanen ne da yammacin Asabar a kusa da shingen tsaron da ya raba bangaren Isira’ila da Falasdinawa.

Hukumar sojin Isira’ila ta ce daya daga cikin dakarunta ya sami raunuka a musayar wutar da aka yi.

Ana samin karuwar tashe-tashen hankula a kusa da kan iyaka a ‘yan kwanakin anan.

XS
SM
MD
LG