Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kimanin mutane dubu bakwai ke dauke da nau’in tarin fuka da baya jin magania Najeriya


Dakin binciken cutar TB
Dakin binciken cutar TB

An yi kiyasin cewa, kimanin mutane dubu bakwai ne ke fama da nau’in cutar tarin fuka da baya jin magani, Babban jami’in rigakafin tarin fuka da cutar kuturta na kasa Dr Mansur Kabir ne ya bayyana hada a wajen wani taron karawa juna sani na kwana biyu da aka shirya wa likitoci da jami’an jinya da kuma ma’aikatan lafiya.

An yi kiyasin cewa, kimanin mutane dubu bakwai ne ke fama da nau’in cutar tarin fuka da baya jin magani, Babban jami’in rigakafin tarin fuka da cutar kuturta na kasa Dr Mansur Kabir ne ya bayyana hada a wajen wani taron karawa juna sani na kwana biyu da aka shirya wa likitoci da jami’an jinya da kuma ma’aikatan lafiya.

Dr Kabir ya bayyana cewa, an sami mutane da dama dauke da nau’in cutar tarin fuka da ake kira MDR a wani bincike da aka gudanar a kasar, abinda ya sa ma’aikatar ta kara kaimi wajen samar da maganin irin wannan nau’in cutar.

Bisa ga cewarshi, ma’aikatar tana aiki tare da hadin guiwar cibiyar bunkasa kasashe ta Amurka USAID da cibiyar shawo kan cututuka ta kasa wajen gano wadanda suke dauke da irin wannan nau’in cutar tarin fukar da kuma samar da maganin da suke bukata domin jinya.

Bisa ga cewar Dr Kabir, cibiya daya rak da ake jinyar wannan cutar a Najeriya ita ce asibitin koyarwa na jami’ar Ibadan yayinda ake kyautata zaton fara aiki a Calabar da Lagos da Zaria da kuma Kano kafin karshen shekarar nan ta dubu biyu da goma sha biyu.

Ya bayyana cewa, an sami jinkiri a fara aiwatar da shirin a sauran sassan Najeriya ne domin tantance cutar da kuma jinyarta na da wuya ainun, yayinda magungunan cutar suke da tsada banda kwarewa da ake bukata wajen aiki da na’urorin jinyar cutar.

Dr. Kabir ya bayyana cewa, kawo yanzu ana samun kimanin masu dauke da cutar dubu dari biyar a duniya kowacce shekara yayinda ake samun nasarar yiwa kashi uku bisa dari jinya har su warke, kasancewa cutar bakuwa ce, kuma magungunan jinyar da ake bukata suna da tsada ainun.

Najeriya ce tafi yawan masu fama da cutar tarin fuka a Afrika inda ake kiyasin cewa, kimanin mutane dubu dari hudu da arba’in suke kamuwa da cutar tarin fuka kowacce shekara a Najeriya. Kwararru sun bayyana cewa, mata da kananan yara suka fi fuskantar hadarin kamuwa da cutar tarin fuka sabili da jikinsu bashi da isasshen karfin yakar cutar.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG