Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cikakken Bayanin Cutar Maleriya Kashi Na Biyar: Wanene Ke Cikin Kasadar Kamuwa Da Ita?


Gwajin wani maganin rigakafin Maleriya a kasar Kenya a watan Nuwambar 2010

Kimanin rabin al'ummar duniya suke cikin kasadar, amma ta fi yin tsanani a kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara

Kimanin rabin al’ummar duniya su na cikin kasadar kamuwa da cutar maleriya. Amma an fi kamuwa da wannan cuta da kuma ganin mace-macen da ta ke haddasawa a kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara. Sauran sassan da wannan cuta ta ke addaba sune Asiya da Latin Amurka. Haka kuma yankin Gabas ta Tsakiya da wasu sassan nahiyar Turai su na ganin wannan cuta amma ba sosai ba. A shekarar 2008, an samu bullar cutar maleriya a kasashe da yankuna 108 na duniya.

Wadanda suka fi kasadar kamuwa da Cutar Maleriya sune:

Na farko, yara kanana a yankunan da babu wannan cuta sosai, wadanda jikinsu bai riga da ya samu garkuwa ba. Akasarin wadanda wannan cuta ta ke kashewa a duniya yara ne kanana.

Na biyu su ne mata masu juna wadanda ba su da kariya a saboda cutar Maleriya tana haddasa barin ciki sosai (Jinsin kwayar cutar Maleriya ta P. falciparum tana iya sanya kashi 60 cikin 100 na matan da suka kamu su yi barin ciki). Haka kuma cutar tana kashe mata masu juna biyu har kashi 10 zuwa kashi 50 cikin 100.

Na uku sune matan dake da kariya amma ba sosai ba a yankunan da cutar Maleriya ta yi tsanani. Maleriya tana iya janyo barin ciki, da rage nauyin jariri, musamman ciki na farko ko na biyu ga wannan macen da ta kamu. Jarirai kimanin dubu 200 ne suke mutuwa kowace shekara a sanadin kamuwa da cutar maleriya da uwayensu suka yi lokacin da suke dauke da cikinsu.

Na hudu, Mata masu juna dake da kariya amma ba cikakkiya ba, suke kuma dauke da kwayar cutar HIV mai haddasa kanjamau ko SIDA su na da kasadar kamuwa da cutar maleriya ko da a yankunan da cutar ba ta yi tsanani ba. Matan da kwayar cutar maleriya ta samu shiga cikin mahaifarsu, su na da kasada babba ta yada kwayar cutar HIV dake jikinsu ga jariran dake cikinsu.

Na biyar, Mutanen dake dauke da kwayar cutar HIV mai haddasa kanjamau ko kuma cutar ta kanjamau su na cikin babbar kasada ta kamuwa da Maleriya idan sauro dake dauke da kwayar cutar ya cije su.

Na shida, Matafiya daga yankunan da babu wannan cuta ta Maleriya su na cikin babbar kasada a saboda jikinsu ba ya da kariya daga wannan cuta.

Na bakwai, Mutane ‘yan asalin wuraren da wannan cuta ta yi tsanani da suka kaura su na zaune a wuraren da babu wannan cuta su na cikin babbar kasadar kamuwa idan sun koma kasashensu domin ziyarar ‘yan’uwa a saboda garkuwar wannan cuta dake jikinsu ta ragu ko kuma ta bace gaba daya.

A cikin kashi na shida, zamu yi bayani a kan yadda ake ganowa da kuma jinyar cutar Maleriya.XS
SM
MD
LG