Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cikakken Bayanin Cutar Maleriya Kashi Na Uku - Yadda Maleriya Take Yaduwa


macen sauro jinsin Anopheles ita ce ke yada cutar maleriya idan ta ciji mutum

Ana iya kamuwa da cutar Maleriya ce kawai ta hanyar cizon macen sauro da ake kira "Anopheles" watau mutum ba zai iya dauka daga wani mutum mai cutar ba

YADDA MALERIYA KE YADUWA:

Ana iya kamuwa da cutar Maleriya ce kawai ta hanyar cizon macen sauro da ake kira "Anopheles." Tsananin cutar, ya dogara a kan irin jinsin kwayar cutar da ta shiga jikin mutum, da yanayin sauron da ya sanya masa kwayar cutar, da yanayin lafiyar jikin shi kansa wanda sauron ya ciza, da kuma muhallin da yake ciki.

Shi kansa sauro jinsin "Anopheles" ya karkasu zuwa wasu kananan jinsunan. Akwai kananan jinsunan sauron "Anopheles" kimanin 20 wadanda suke da matukar muhimmanci a yankuna dabam-dabam na duniya. Dukkan kananan jinsuna wannan sauro mai yada cutar Maleriya dake da muhimmanci, ba su cizon mutane sai da daddare. Su na kiwo a duk wani dan gulbin da ruwa ke taruwa, kamar a lambatu, ko ramin dake gefen hanya, ko gonakin shinkafa, ko fadamu da makamantansu.

Kamuwa da cutar Maleriya tana yin tsanani a inda wannan sauro ya samu sukunin jimawa, watau ya samu wadataccen lokacin da wannan kwayar cuta zata gama girma a cikin wannan sauro kafin ya ciji mutum ya zuba masa. Haka kuma tana yin tsanani a wuraren da sauron ya kan gwammaci cizon mutane a maimakon dabbobi. Alal misali, tsawon rayuwar kananan jinsunan sauro mai yada Maleriya a nahiyar Afirka da kuma yadda sukan gwammace su ciji dan Adam a maimakon dabbobi, sune suka sa fiye da kashi 85 cikin 100 na dukkan wadanda cutar Maleriya take kashewa, ‘yan Afirka ne.

Wani abu mai muhimmanci kuma, shi ne irin kariyar da dan Adama yake da ita ta garkuwar jiki, musamman ma a tsakanin balagaggun mutane a yankunan da cutar take da tsanani da kuma inda ake fama da ita sosai amma ba ta yi tsanani ainun ba. Wannan kariya tana samuwa ne a saboda yawan kama cutar da mutum zai yi, abinda ke sa tsananinta ya ragu a jiki, amma kuma ba a samun kariya baki daya. A saboda haka ne mafi yawan wadanda cutar Maleriya take kashewa a nahiyar Afirka, yara ne kanana wadanda jikinsu bai samu wannan kariya ba tukuna.

Amma kuma a yankunan da wannan cuta ba ta yi tsanani ba, kuma mutane ba su da kariyar garkuwar jiki, tana iya kashe yara da manya, maza da mata.

Haka kuma, kamuwa da wannan cuta tana dogara a kan yanayi wanda zai iya tantance yawan sauro ko kuma rayuwarsu ma, kamar yawan ruwan sama, ko lokacin sanyi ko na zafi, har ma da yawan tururi dake cikin iskar shaka. A wasu wuraren, ana kamuwa da wannan cuta ta Maleriya ne lokaci-lokaci, inda ta fi yawa a lokacin damina, da kuma ‘yan watanni kadan a bayan daminar.

A kan samu barkewar annobar cutar Maleriya idan yanayi ya sauya ya zamo mai kyau ga sauro a wuraren da mutane ba su da kariyar garkuwar jiki ga wannan cuta ta Maleriya. Haka kuma, ana samun annobar cutar idan mutane marasa kariyar garkuwar jiki suka kaura zuwa yankunan da wannan cuta ta yi kanta, alal misali idan masu neman aiki ko ‘yan gudun hijira daga inda ba a saba da sauro ba suka koma inda sauro ke cin karensa babu babbaka.

A kashi na hudu na wannan bayanin, zamu duba alamun wannan cuta ta Maleriya. A biyo mu domin a karu.

Duba kashi na Farko kan Asalin Cutar Maleriya da Bayaninta

Duba Kashi na Biyu kan Abinda Ke Janyo Cutar Maleriya

XS
SM
MD
LG