Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cikin Wannan Shekarar 'Yanjarida Hamsin Suka Rasa Rayukansu A Bakin Aiki


Almigdad Mojalli na Muryar Amurka yana cikin 'yanjarida hamsin a duk fadin duniya da suka rasa rayukansu yayinda da suke bakin aiki a wannan shekara mai shudewa

A wannan shekarar mai karewa ta 2016, an bada kiddidigar dake nuna cewa kusan ‘yanjaridu hamsin suka rasa rayukkansu a bakin aiki a shekarar – ciki harda wani ma’aikacin gidan rediyon nan namu na Muryar Amurka mai suna Almigdad Mojalli, wanda ya rasa ransa a kasar Yemen inda yaje dauko labarin kazamin yakin da ya barke a can.

Mojalli na daya daga cikin ‘yanjaridu shidda da aka kashe a kasar ta Yamen, abinda yassa Yemen din, tareda Iraq, suka zo a matsayi na biyu na kasashen da aka fi asaran rayukkan ‘yanjaridu a bana, a cewar wani rahoto da Kungiyar kare Hakokin ‘Yanjaridu ta Duniya ta sako.

Duka-duka jimillar ‘yanjaridu 48 suka rasa rayukkansu a bakin aiki a wannan shekarar ta 2016, galibinsu a kasashen Syria, Iraq, Yemen, Libya da Afghanistan.

Sai dai kuma duk da yawansu, basu kai yawan wadanda aka hallaka a shekarar da ta gabata ba ta 2015 ba, lokacinda aka kashe ‘yanjaridu 72.

A nahiyar Afrika, jimillar ‘yanjaridu 6 aka kashe, wasu 41 na tsare a gidajen kurkuku daban-daban.

A tsakanin kasashen na Afrika, ba inda aka yi wa manema labarai lahani kamar Somalia inda aka kashe guda ukku a wannan shekarar.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG