Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Clinton da Trump Yau Sun Maida Hankulansu Ne Akan Neman Zabe A Jihar Florida


Hillary Clinton da Donald Trump dukansu 'yan takara
Hillary Clinton da Donald Trump dukansu 'yan takara

Yanzu ana iya cewa aski ya kawo gaban goshi a zaben shugaban Amurka da 'yan majalisun tarayya da wasu gwamnoni da 'yan majalisun wasu jihohin

Sauran makonni 2 a kaiga ranar zabe. ‘Yan takaran shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donald Trump da ta Democrat Hillary Clinton sun maida hankali akan yakin neman zabe yau Talata a jahar Florida, jihar da ke da tasiri sosai ga ‘yan takarar a kokarin da suke yi na samun shugabancin Amurka.

Jihar Florida dake kudu maso gabashin Amurka, ita ce mafi girma a wannan banagren inda ake gogawa akan zaben na ranar 8 ga wata Nuwamba. Tana da wakilai masu zaben shugaban kasa 29 daga cikin 270 din da dan takara ke bukata don cin zabe. Kasar Amurka na gudanar da zaben shugaban kasa duk bayan shekaru 4 ta hannun wakilai, dake da jihohin da suka fi yawan al’umma da zasu taimaka a zaben, maimakon yawan kuri’un jama.

Ra’ayyoyuin jama’a a Florida sun nuna cewa Clinton, tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka dake sa ran zama mace shugaba ta farko a amurka, tana gaban Trump da kusan maki 4 a jihar, inda mutane miliyan 1.6 suka riga suka kada kuri’unsu a mazabunsu.

XS
SM
MD
LG