Accessibility links

Clinton Ta Yi Gangami Mafi Girma a New York


Sakatariyar harkokin wajen Amurka,Hillary Clinton

Tun bayan da ta bayyana aniyar ta sake tsayawa neman takarar shugabancin kasar Amurka, tsohuwar Sakatariyar harkokin wajen kasar, a yau Asabar Hillary Clinton ta yi wani gangami mafi girma a birnin New York.

‘Yar takar neman shugabancin kasar Amurka, a karkashin jam’iyyar Democrat, Hilary Clinton, ta gudanar da gangami mafi girma a New York inda ta yi wani jawabi mai cike da barkwanci da alkawuran samar da daidaito a tsakanin al’umar kasar.

A jawabin nata, wanda aka nuna a gidajen talbijin din kasar, Clinton ta gayawa dubban mutane cewa ta tsaya neman takarar shugabancin kasar ne domin Amurkawa.

Ta kara da cewa babu yadda Amurka za ta ci gaba, idan Amurkawa ba su samu ci gaba ba, inda ta kara da cewa mulkin dimokradiyya ba na masu hanu da shuni ne kadai ba.

Clinton, wacce ta rike mukamin Sakatariyar harkokin wajen Amurkan, ta kuma gayawa dubban mutane da suka halarci gangamin cewa ita tafi kowa sanin matsalolin Amurkawa.

An dai ga dubban mutane suna ta kiran sunanta a yayin gangamin suna masu jinjina mata.

A gobe Lahadi a ke sa ran za ta yada zango a jahar Iowa inda za ta ci gaba yakin neman zaben nata.

XS
SM
MD
LG