A yau Litinin hukumomi a Korea ta Kudu, suka ce mutum 231 suka sake kamu wa da cutar coronavirus, lamarin da ya kai adadin masu dauke da cutar zuwa 833.
Hukumomin har ila yau sun bayyana cewa an samu karin mutum biyu da suka mutu – kuma hakan na nufin mutum bakwai kenan suka rasa rayukansu a kasar baki daya.
Gabanin fitar da wannan sanarwa a yau Litinin, Korea ta Kudu ta tsaurara yaki da cutar zuwa mataki na kololuwa, sannan Shugaba Moon Jae-in ya yi kira ga jami’an
lafiyan kasar da kada su yi wata-wata wajen daukan duk matakan da za su iya dakile yaduwar wannan cuta.
Daga cikin matakan da aka dauka, hukumomin sun jinkirta bude makarantu bayan hutun da aka yi, sannan an rage zirga-zirgar motocin sufuri mallakar gwamnati, cewar mataimakin Ministan ma’aikatar lafiya da walwalar jama’a Kim Kan-lip
Ya ce, “idan ba mu dakile yaduwar wannan cuta ba musamman a yankin Daegu, akwai yiwuwar ta bazu a zuwa sauran sassan kasar.”
Ita dai Korea ta Kudu, ita ce kasar da ta fi kowace yawan adadin wadanda suka kamu da cutar ta coronavirus, baya ga China.
Facebook Forum