Yayin da ake samun karuwar cutar COVID-19 a birnin Los Angeles, magajin garin birnin Eric Garcetti ya sanar da yiwuwar sake kulle birnin, makwanni kalilan bayan da hukumar birnin ta sassauta dokar hana zirga zirga.
A gidan yarin jihar, lamarin ya rincabe, inda hukumomin jihar California ke tunanin sakin fursunoni kimanin 8,000 masu kananan laifi.
Jihar California na cigaba da kasancewa kan gaba wurin yawan masu cutar, inda aka tabbatar da kimanin mutum dubu 400 sun kamu da cutar.
Domin sassauta wannan matsala, jami’ai sun ce suna tunanin sakin fursunoni dubu takwas masu kananan laifi da ya rage musu kasa da kwanaki 180 su gama zaman gidan yarin.
Masu sama da shekaru 30 da basu da cikakken koshin lafiya ne za a fara sakewa.
Kimanin ‘yan gidan yari dubu uku ne a California aka tabbatar da sun kamu da COVID-19, kana akalla mutum goma a ciki sun mutu.
Masu suka sun ce musayar fursunoni shine ya yi sanadin bazuwar cutar a gidajen yari. Tun lokacin ne jihar ta maye gurbin babban jami’in lafiya na gidajen yari.
Wasu da suka taba zaman gidan yari sun bayyana abubuwa da suka gani a lokacin barkewar annobar.
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 25, 2023
Mawakiya Yar Najeriya Ta Yi Tarihi A Bikin Bada Lambar Yabo Na Oscar
-
Janairu 13, 2023
Lisa Marie Presley, Diyar Mawaki Elvis Ta Rasu
-
Janairu 11, 2023
Ana Tsaftace Yankunan Da Mahaukaciyar Guguwa Ta Ratsa A California
Facebook Forum