Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: "Facebook Zai Taimaki Najeriya Yaki Da Labaran Bogi"


Lai Mohammed, Nigeria Minister of Information and Culture

Kamfanin sada zumunta na Facebook, ya ce zai taimaki hukumomin Najeriya wajen yaki da masu yada labaran karya game da bullar cutar coronavirus a kasar.

Ministan Labarai da Al'adu na Najeriya, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a babban birnin tarayya Abuja.

A cewarsa, Facebook ya bukaci hukumomin Najeriyar da su kai rahoton labarin da suke ganin babu gaskiya a ciki da kuma duk wani na batanci akan shafukan “Instagram” don a yi gaggawar sauke su.

Lai Mohammed ya kuma ba da tabbacin cewa akwai isassun kayayyakin gano wa da kuma yakar cutar.

A karshen makon nan ne hukumomin Najeriya suka bayyana bullar cutar a kasar, bayan da aka gano wani dan Italiya dauke da ita

Lai Mohammed ya ce, sun san cewa a irin wannan lokacin za a yi ta yada labaran karya da jita-jita, don haka suna bukatan ‘yan Najeriya da su yi hakuri, kuma su yi hattara kar su fada tarkon masu watsa labaran karya.

Minister of Information and Culture, Lai Muhammed
Minister of Information and Culture, Lai Muhammed

Babban Sakatare a ma'aikatar kiwon lafiya ta Najeriya, Abdulazeez Mashi Abdullahi, ya yi nazarin yadda cutar da kuma matakan kariya da suka dauka akan hanyoyin dakile yaduwar cutar.

Mashi ya ce, a cikin binciken su, sun gano cewa cutar tana iya zama a jikin mutum har na kwanaki 14 kafin ta bayyana ta hanyar zazzabi mai zafi.

Ya kuma ce sun tanadi kayan gwaji da za su tabbatar da lafiyar matafiyi da ke sauka a filin jiragen sama guda biyar da ake da su a kasar.

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG