Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Covid-19: Farashin Danyen Mai Ya Fadi


Allurar rigakafin Covid 19
Allurar rigakafin Covid 19

Farashin Danyen Mai Ya Fadi Kasa da Dala 70 Yayin da Haramcin Balaguro ke Barazana Faruwa Sakamakon Nau’in Omicron na cutar coronavirus.

Kasuwar danyen mai na ci gaba da fuskantar barazana sakamakon gano sabon nau’in cutar korona birus nau’in Omicron, wanda ya sanya farashin danyen mai raguwa kasa da dala 70 kan kowacce ganga.

Baya ga barazanar da sabon nau’in cutar ke yi ga kasuwar man fetur, kungiyar kula da ayukan sufurin jiragen sama ta duniya wato IATA, ta yi gargadin cewa matakin da kasashe suka fara sanarwar dauka game da nau’in cutar korona birus na Omicron ya fara haifar da barazana ga farfadowar bangaren jigilar jiragen sama.

A halin yanzu farashin danyen mai samfurin Brent na Najeriya na kan dala 68.88 kan kowacce ganga yayin da samfurin West Texas Intermediate wato WTI, shi ma an rufe farashinsa da raguwar kaso 0.92 cikin 100 a kan dala 65.57.

Danyen mai na Najeriya farashin samfurin Bonny Light ya rufe kan dala 69.81 kan kowacce ganga, wanda ke nuna raguwar kaso 5 da digo 05 cikin 100.

La’akari da sabon nau’in kwayar cutar korona birus da aka tabbatar da cewa tana turjiya ga maganin rigakafi, farashin danyen man ya samu koma baya sosai a makon da ya gabata.

Kamfanin zuba jari da bankin kasa-da-kasa na Morgan Stanley na Amurka ya ce la’akari da wannan yanayi, tabbas a game da abun da nau’in Omicron ka iya halfar a duniya, ana tsammanin kungiyar OPEC mai kula da kasashen masu albarkatun man fetur za ta kawar da burinta na habaka aiki hako mai a cikin watan Janairu shekarar 2022 tare da ci gaba da daidaita ka’idojinta, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Masanin tattlin arziki, Kasim Garba Kurfi, ya bayyana cewa akwai fargabar cewa idan aka sami tasgaro a kasuwar danyen mai, akwai yiyuwar hakan zai yi illa ga tattalin arzikin Najeriya, wanda ke samun makudan kudaden shiga daga fitar da danyen mai.

A halin yanzu dai Najeriya ta sami mutum uku masu dauke da cutar korona birus nau’in Omicron kuma hukumar yaki da cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta ce an gano su ne bayan tattara samfurin gwajin kwana biyu da aka kayyade ga duk matafiya da suka shigo Najeriya.

Sabbin masu dauke da nau’in Omicron din sun shigo Najeriya ne a cikin makon da ya gabata kuma gwamnati ta na bita don tabbatar da wadanda suka kamu da cutar sun kebe kansu, an kai zuwa asibiti don kulawa ta musamman, gano wadanda suka yi mu’amala da masu dauke da sabon nau’in Omicron ta hanyar tuntubar juna da sauran ayyukan tabbatar da kare sauran yan kasar.

Haka kuma gwamnati na shirye-shiryen sanar da kasar da aka yi balaguron daga cikinsu da cutar Omicron bisa tanadin dokokin kiwon lafiya na duniya, in ji hukumar NCDC.

Haka kuma, kafin samun bullar cutar COVID-19, sashen mai na Najeriya gabadaya ya kai kusan kaso tara cikin 100 na babban abin da ake samu a cikin gida wato GDP.

Kazalika tsakanin watan Oktoba da Disambar shekarar 2020, masana'antar man fetur ta Najeriya ta ba da gudummawar kaso 5 da difo 9 cikin 100 ga jimillar GDP na kasar.

Alkaluman kididdiga sun yi nuni da cewa Najeriya dai na daya daga cikin kasashe masu arzikin man fetur a duniya kuma a farkon shekarar 2020, yawan man da take hakowa a kullum ya haura ganga miliyan biyu.

Bayan haka, aikin hako man ya ragu zuwa ganga miliyan 1 da dubu 140 a kowace rana a cikin watan Janairun shekarar 2021, wanda ya kasance mafi karancin kima da aka samu a cikin 'yan shekarun nan.

Alkaluman kididdiga sun yi nuni da cewa an sami mafi karancin aikin samar da mai a kowacce rana a Najeriya a cikin watanni uku na farkon shekarar 2021.

Duk da cewa faduwar farashin man har yanzu bai yi kasa da ma'auni da aka yi amfani da shi wajen gabatar da kasafin kudin shekarar 2022 ba, masanin tattalin arziki, Kasim Garba Kurfi ya bayyana fargabar cewa duk wani yunkuri na yin kulle-kulle a duniya zai yi illa ga tattalin arzikin kasashe masu dogaro ga kudadden shigan man fetur kamar na Najeriya.

Tun kafin samun bullar cutar korona birus ne masana tattalin arziki da sauran masu ruwa da tsaki a faninin bunkasa tattalin arzikin Najeriya ke yin kira ga kasar da ta karkatar da akalar tattalin arzikinta daga dogaro kacokan ga bangaren man fetur zuwa ga aikin noma, fasahar zamani, sarrafa abane amfanin yan kasa a cikin gida da dai sauransu.

XS
SM
MD
LG