Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

WHO Ta Ce Omicron, Sabon Nau'in COVID-19 Da Ya Bulla A Afurka Ta Kudu, Na Iya Saurin Yaduwa


Tedros Gebreyesus
Tedros Gebreyesus

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) jiya Jumma'a Jumma'a ta ayyana nau'in B.1.1.529 da aka gano a Afirka ta Kudu a matsayin SARS-CoV-2 , ta na mai cewa nau'in yana iya yaduwa cikin sauri fiye da sauran nau'ikan.

Alamu na farko na nuna cewa akwai karuwar kasadar sake kamuwa da cutar, kuma mummunan canji ya yi ta aukuwa game da yanayin COVID-19," in ji sanarwar, bayan wani taron sirri na ƙwararrun masana masu zaman kansu waɗanda suka sake nazarin bayanan.

Masu kasuwa da cutar sun karu sosai a 'yan makonnin nan, wanda ya zo daidai da gano nau'in da aka bayyana a matsayin omicron, in ji WHO.

Omicron shi ne nau’i na biyar da aka ayyana da hakan. WHO ta ce "An gano wannan nau'in da sauri sosai fiya da sauran nau'ukan da su ka yada da sauri, wannan hakan ke nuna cewa wannan nau'in na iya fin sauran saurin yaduwa, wanda hakan ke nuna cewa wannan nau’in na iya bazuwa da sauri," in ji WHO.

Gwajin PCR na yanzu yana ci gaba da nasarar gano wannan nau’in , in ji hukumar ta WHO.

Tun da farko, hukumar ta WHO ta gargadi kasashe da su guji yin gaggawar sanya takunkumin tafiye-tafiye da ke da alaƙa da nau’in COVID-19, tana mai cewa ya kamata su ɗauki matakan “kiyaye haɗari da amfani da bayanan kimiyya.”

Hukumomin duniya sun mayar da martani da fargaba game da sabon nau’in da aka gano a Afirka ta Kudu din, ta yadda kungiyar Tarayyar Turai (EU) da Burtaniya ke sahun kasashen da su ka dau matakan takaita shigowa ta kan iyakokinsu yayin da masana kimiyya ke kokarin gano ko wannan nau’in zai fi karfin allurar rigakafi.

"A wannan lokacin, ana yin taka tsantsan game da aiwatar da matakan balaguro," in ji kakakin WHO Christian Lindmeier a wani taron Majalisar Dinkin Duniya a Geneva. "WHO ta ba da shawarar cewa kasashe su ci gaba da yin amfani da tsarin takaita kasada da kuma amfani da bayanan kimiyya yayin aiwatar da matakan balaguron."

Yanzu haka Shugabannin Tarayyar Turai sun yanke shawarar dakatar da tafiye-tafiye daga kudancin Afirka bayan gano wannan sabon nau'in COVID-19, in ji ofishin shugabar Tarayyar Turai a ranar Juma'a.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG