Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: Najeriya Ta Saka Afirka Ta Kudu Cikin Kasashen Da Ta Haramtawa Matafiyansu Shiga Kasar


Lokacin da aka yi shugaba Buhari allurar rigakafin COVID-19 (Twitter/Presidency)

Afirka ta Kudu ita ce kasar da ta fi yawan wadanda suka kamu da cutar ta COVID-19 a nahiyar Afirka.

Hukumomi a Najeriya sun kara Afirka ta Kudu cikin jerin kasashen da ta hana matafiyansu shiga kasar saboda yadda annobar COVID-19 ta yi kamari a kasashensu.

A ranar 4 ga watan Mayu Najeriyar ta hana matafiya daga India, Brazil da Turkiyya shiga kasar, a wani mataki na kaucewa yada cutar coronavirus.

Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin da shugaban kasa ya kafa don yaki da cutar ta COVID-19, Boss Mustapha ne ya bayyana daukan matakin a taron manema labarai da kwamitin ya gudanar a Abuja kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka ruwaito.

Mustapha ya ce sun kuma kara tsawaita haramcin da wata guda ga kasashen uku bayan nazarin da suka yi kan yadda al’amura ke gudana a kasashen.

Wannan mataki na zuwa ne yayin da Najeriyar ta samu karin sabbin mutum 65 da suka kamu da cutar a ranar Litinin.

Mutum 167, 532 aka tabbatar sun kamu da cutar, sannan 2,119 suka mutu tun bayan bullar cutar a kasar wacce ta fi kowacce kasa yawan al’uma a Afirka.

A Afirka ta Kudu kuwa, Mutum 1, 928, 897 suka kamu da cutar, sannan 59,990 suka mutu kamar yadda alkaluman cibiyar John Hopkins ta suka nuna.

Afirka ta Kudu ita ce kasar da ta fi yawan wadanda suka kamu da cutar a nahiyar Afirka.

Matakan da hukumomin Najeriyar ke dauka na kaucewa yaduwar cutar na zuwa ne, a daidai lokacin da kasar ke kimtsawa kan yiwuwar samun tashin cutar a karo na uku.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG