Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19 Ta Kashe Shahararren Dan Najeriya Ba-Amurke


Wani shahararren dan Najeriya kuma Ba-Amurke, dan kasuwa Jonathan Adewumi, ya mutu a birnin New York sakamakon cutar COVID-19.

Adewumi na da hadakar mallakar shahararren gidan abinci mai suna “Amarachi” da ke a Brooklyn. Gidan cin abincin wata babbar matattara ce da wurin shakatawa ga ‘yan Afirka dake yankin.

Adewumi ya kasance "babban jakadan Afirka a wajen taimako da yada al'adu da tarihi.

Baya ga gidan abincin, Adewumi ya kan dauki nauyin shirya bikin fina-finai na Najeriya, sannan yana da kamfanin tafiye-tafiye, wanda yake taimakawa masu yawon shakatawa damar zuwa yankuna daban-daban na Afirka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG