Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: Za a Fara Bin Gida-gida Don Yin Gwaji a Kano


Gwamnatin jihar Kano hadin gwiwa da hukumar lafiya ta duniya WHO sun yi tanadin ma’aikatan kiwon lafiya kimanin 4,000 domin aiwatar da tsarin gwajin cutar Coronavirus na gida-gida.

Cikin wata sanarwa, gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana cewa za a bi gida-gida a birni da kuma kewayen Kano domin gwada mutane domin tabbatar da cewa, al’uma ba sa dauke da wannan cutar.

Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da kwamitin yaki da cutar Corona a jihar Kano ya fitar da sanarwar warkewar mutane uku daga cikin kimanin 400 masu dauke da cutar a jihar Kano.

Dr. Tijjani Hussain da ke zaman mai shirya tsare-tsaren da ake bi wajen yaki da cutar a jihar ya yi wa Muryar Amurka karin haske kan wannan tsarin.

“Idan jami’an suka shiga gidajen mutane kuma suka ga alamun akwai mai cutar, sai sun kira ma’aikatanmu wadanda ke da hurumin daukar samfurin mutane domin su zo su yi musu gwajin.”

A cewar hukumar dakile cututtuka ta Najeriya, NCDC ya zuwa yanzu mutum 11 ne suka rasa rayukansu a jihar ta Kano sakamakon wannan cutar ta Coronavirus.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG