Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cuba ta Zargin Amurka da Gangan ta yi Karya a Kan harin wata cutar da ba a gano sanadinta ba


Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump

Ministan harkokin wajen Cuba ya zargin Amurka da gangan ta yi karya game da harin wata cutar da ba a gano sanadinta ba a kan jami’an diplomaisyar Amurka a Cuba

A wani taron manema labarai na musamman a cibiyar yan jarida ta kasa a nan Washington a jiya Alhamis, Bruno Rodriguez ya yi kira ga gwamnatin Trump da ta fadi gaskiyar maganar ko kuma ta gabatar da shaidarta.


Yace ina fadin cewa babu wani hari da aka kai. Babu wani abu da gangan da ya faru. Kuma babu wani takamaiman abu da ya faru. Yace idan gwamnatin Amurka tana da wani bayani sabanin haka ta kawo shaidarta.


Amurka ta rage yawan ma’aikatarta a ofishin jakadancinta a Havana da kashi sittin cikin dari a wani mataki da ya biyo bayan wannan abu kuma ta kori wasu jami’an diplomasiyar Cuba 17 daga ofishin jakadancin kasar Cuba a nan Washington.


Amurka ta kuma gargadi Amerikawa a kan tafiya zuwa Cuba kana ta dakatar da bada biza ga yan kasar Cuba a Havana.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG