Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Annobar Cutar Coronavirus Na Sauya Harkokin Siyasa a Afrika Ta Kudu


Yaduwar annobar cutar coronavirus ta sauya al’amura baki daya a kasar Afrika ta Kudu, ciki har da turka-turkar siyasar bangaranci.

A yayin da adadin wadanda suka kamu da cutar coronavirus ya zarta 100 a kasar, hakan ya kawo wani hadin kan siyasa daga bangaren shugaban kasar Cyril Ramaphosa da manyan abokan adawar siyasarsa.

Shugaban kasar ya tsaya kafada-da-kafada da abokan hamayyarsa a wani taron manema labarai a Cape Town, duk da yake sun tsaya nesa da junansu, kuma sun taba juna ne kawai da gwiwar hannu.

Cikin murmushi Ramaphosa yayi jawabi ga manema labarai, inda ya ce sun ajiye duk wasu bambance-bambance da ke tsakanin su domin yakar annobar ta COVID-19.

Ramaphosa ya ce, shugabannin siyasar sun kuma tattauna akan lamuran da suka shafi rashin raba daidai, da zai iya shafar kokarin yaki da cutar.

‘Yan kasar da dama masu karamin karfi basu da muhimman ababen bukata a gidajensu, wanda hakan ke sa suna dogara da ayyukan da ake cunkoso kamar sufuri da zirga-zirga, inda aka fi saukin kamuwa da cutar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG