Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ebola Na Ci Gaba Da Hallaka Mutane A Congo-Kinshasa


Likita

An sami mutuwar karin wani mutum guda da ake jin cutar Ebola ce ta hallaka shi a kasar Congo-Kinshasha, abinda zai sa jimillar mutanen da cutar ta kashe zuwa 12 ke nan.

Wannan mutum na baya-baya da aka rasa, mutumen wani kauye ne dake yankin Iboko dake lardin Equateur a arewa-maso-yammacin kasar.

Ko bayan mamacin, har ila yau ance akwai wasu mutane hudu da suka kamu da cutar a yankin, wanda wannan ke nufin ke nan yanzu akwai jimillar mutane 35 dake dauke da Ebola a kasar ta Congo.

A yau Litinin ne dai aka shirya fara gudanar da rigakafin gujewa kamuwa da cutar a yankunan Iboko da Bikoro dake lardin na Equateur.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG