Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Tarin Fuka a Nijeriya Ta Wuce Yadda Ake Sammani

Hoton kirjin mai fama da cutar tarin fuka
Hoton kirjin mai fama da cutar tarin fuka

Faman da Nijeriya take ciki da cutar tarin fuka ya fi yadda ake sammani. An bincika cewa zai zama kamar sau uku fiye da yadda kungiyar lafiya ta duniya ta fadi da kuma sau biyar fiye da wadda akayi rahoto a kungiyar kiyaye cutar tarin fuka da kuturta, inji ministan lafiya na jiha, Dr Khaliru Alhassan.

Kungiyar lafiya ta duniya ta kimmanta kashi 180,000 na masu fama da cutar fuka a Nijeriya kowacce shekara. Kungiyar tace Nijeriya tana cikin kasashe 11 daga 22 wadanda suke da cutar tarin fuka da yawa wanda yakai kashi 80% na dukan duniya.

Yayinda yake ganawa gameda ranar duniya ta cutar fuka a Abuja, Dr. Alhassan yace damuwar Nijeriya ta karu ne tawurin haduwar cutar fuka da kuma kanjamau.

Binciken cutar tarin fuka da aka yi ta nuna marasa lafiya kashi 4.3 ke bukatar shan magani bayan wanda suka sha bai yi masu aiki ba.

Kamar yanzu marasa lafiya 523 sun sami magani kan irin kwayar cutar tarin fuka dake kin magani, da kuma kusan guda 60 sun sami sami lafiya, bisaga kungiyar cutar tarin fuka ta kasa da kuma kauda cutar kuturta.

Kusan marasa lafiya 89 wadanda aka kawo domin maganin cutar tarin fuka an same su da cutar kanjamau a 2013, daga kashi 10 a 2006, bisaga binciken ma’aikatar lafiya ta kasa.

Inji kungiyar lafiya, an kafa wani na’ura mai suna GeneXpert, da yake taimaka tantace kwayar cutar tarin fuka a jiki, ama wurare 52 ne kawai ke amfani da shi a dukan Nijeriya. GeneXpert yana gano kwayar dake kawo cutar tarin fuka kuma yana hana jiki yaki amfani da magani, kuma ana tura shi ya kara ganin inda cutar yake da kuma yaduwarta.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG