Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cututukan Da Ake Bukatar Yiwa Yara Rigakafi A Shekaru Biyar Na Farko-Kashi Na Daya


Wani yaro ana yi mashi allurar rigakafi

Kwararru a fannin magunguna da ayyukan jinya sun bayyana jerin cututukan da ake bukatar yiwa kanannan yara rigakafi kafin su cika shekaru biyar domin kare su

Ciwon Hakarkari Na Kananan Yara
Ciwon hakarkari shine ciwon da yafi kashe kananan yara a fadin duniya baki daya. Hukumar lafiya ta duniya ta ce, ciwon hakarkari yana kashe kimanin kananan yara miliyan daya da dubu dari biyu dake kasa da shekaru biyar kowacce, kuma shine sanadin mutuwar kashi 18% na kananan yara kasa da shekaru biyar a fadin duniya.

Likitoci suka ce a na iya kare ciwon hakarkari da rigakafi, da abinci mai kyau da kuma tsabtace muhalli. Yaran da suka kamu da ciwon kuma,, za a iya jinyar kwayar cutar da suke dauke da ita ta wajen basu magani.

Tarin fuka
Tarin fuka kwayar cuta ce mai yaduwa da ke kai ga tari marar iyaka. Masu ilimi sun ce ko da yake kowa na iya kamuwa da cutar amma tafi yawa da muni tsakanin kananan yara; kuma likitoci sun bayyana cewa yafi muni a jarirai. A na iya kare shi da rigakafi.

Bakon dauro
Bakon dauro babbar cutar viral ce mai yaduwa da ke da hatsari da kuma muni, ya na iya sa kananan yara su makance ko kuma su mutu. Cuta ce mai yaduwa da illa wadda a ke samu daga kwayar kwayar cuta da take yawo a iska. Tana daya daga cikin cututukan da ke kisan yara. Yanzu ana iya maganin kamuwa daga cutar ta wajen yiwa yara rigakafi.

Shan -inna
Wannan cuta ce mai yaduwa, da ake samun ta daga kwayar cuta dake shafar kananan yara kasa da shekaru biyar. Ciwon r shan-inna yana shafar jijiyoyi ne, kuma takan busar da jijiyoyin cikin karamin lokaci.

Kwayar cutar takan shiga jiki ta baki ne, sannan ta yadu a cikin hanji.Farkon alamun sune shawara, gajiya, ciwon kai, amai, kumburin wuya da zafin jiki. Binciken Hukumar lafiya ta duniya ya nuna cewa daya daga 200 da ke dauke da cutar kan kai ga shankewar jiki musamma a kafafuwa. A cikin shanyewar kusan kashi 5% zuwa kashi 10% na iya mutuwa. Ana kare kamuwa da cutar ta wurin rigakafi

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG