Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijeriya ta Hada Hannu da Kungiyar Lafiya ta Duniya Kan Kiwon Lafiya


Kungiyar Lafiya ta Duniya, WHO
Kungiyar Lafiya ta Duniya, WHO

A sabon kokarin da zai inganta yanayin kula da lafiya, gwamnatin tarayya da kungiyar lafiya ta duniya suna shirya sabobin hanyoyin hadin kai mai dorewa a kasar.

A sabon kokarin da zai inganta yanayin kula da lafiya, gwamnatin tarayya da kungiyar lafiya ta duniya suna shirya sabobin hanyoyin hadin kai mai dorewa a kasar.

Yayinda yake magana a ganawar Salon Hadin kai na Kasa (CSS) II a Abuja, wanda kungiyar lafiya ta duniya ta shirya, ministan lafiya, Prof. Onyebuchi Chukwu yace wannan sabon shirin ya zama da muhimmanci ganin cewa gwamnati ita kadai ba zata iya tanada dukan bukatun lafiya na ‘yan kasa ba.

A fadar Chukwu, wannan shiri na CCS II yana da mahimmanci kwarai da gaske wajen inganta dangantakar aiki tsakanin gwamnati da kungiyar lafiya ta duniya domin inganta yaki da kawar da cututtuka cikin kasar, ya kara da cewa, wannan ya ba gwamnati damar kirkiro da hanyoyi masu dorewa na inganta lafiyar jama’arta.

Wakilin Kungiyar lafiya ta duniya, DR Gama Vaz yace: “wannan shirin ya bayyana hanyoyin da shirin Lafiya na Kasa, ya baiyyana irin shirin kungiyar lafiya ta duniya wajen hada hannu da kungiyar lafiya ta kasa da kuma daidaita shirye-shiryen ta a kasar.” Vaz kuma ya kara da da cewa shirin zai taimaki gwamnati yin aminci cikin harkokin kiwon lafiya, ya karfafa tsare tsare musamman ma na kananan asibotoci ya kuma fifta sassan dake da muhimmanci, ya kuma karfafa hadin gwima da tafiyar da kayan aiki.

Yayinda yake baiyyana shirin, yace shiri ya kunshi bayanai na maida martani daga shirin kungiyar lafiya ta duniya da kuma kungiyoyi na waje dake da hannu a cikin shirin.
Yayinda take baiyyana sakamakon ga wadanda ke da hannu a cikin shirin, wata mai bada shawara, Dr Lucy Idoko ta lura cewa, “Wannan bayanin ya nuna cewa kungiyar lafiya ta duniya ta wurin.gudanar da shirn CCS II ta tallafa kwarai wajen karfafa inganci cikin kiwon lafiya wanda ya yi sanadiyyar ci gaba wajen rigakafin shan inna a Nijeriya da kuma Karin samun rigakafi a kasar."

Idoko ta ce, “An lura da kalubala a sassan tanajin cigaba, daidaita kawarda cutar shan inna da kuma wasu sassan wadanda suka hada da samun kwararrun ma’aikatan lafiya.” Direkta na kungiyar lafiya ta duniya, Dr Eileen Pitit-Mshana ne ya bayas da bayyanin binciken cikin gidan da aka gudanas.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG