Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Dan Gari: Tarihin Garin Janguza, Kano


A wannan makon gidan rediyon jihar Kano ya lalubo tarihin garin Janguza da ke karamar hukumar Tofa a jihar Kano.

Garin Janguza dai shine mai masaukin wani babban barikin soja mai suna Janguza da kuma babban katafaren kurkurun da gwamnatin tarayya ke ginawa a gefen babban titin da ya tashi daga birnin Kano zuwa garin Gwarzo daga kudu.

Garin Janguza dai gari ne mai ganuwa da wasu fatake suka kafa shi shekaru fiye da 300 da suka gabata.

Dahiru Hudu Janguzu, wakilin mai garin Janguza Alhaji Hudu Yakubu, ya ce a baya fatake na dauko kaya da jakuna daga yammacin Kano su kai garin, har suka sami mazauni.

Ya kara da cewa garin wanda yanayin kasarsa Ja ne, ya samo asali ne daga wani basarake mai suna Guza, yadda aka sami sunan kenan “Janguza.” A cewar ‘yan fadarsa, idan Basaraken ya fita zagaya iyakokin garin akan ga macizai, kunkuru da damo suna bin sa a baya amma ya fi zama a wani makwancinsa da ke yamma da garin, daga baya fatake suka same shi a garin.

Malam Hudu ya ce bayan fatauci garin Janguza ya yi fice a harkar saka, a yanzu kuma ana noma, sana’o’i da ilimin boko.

Saurari cikakken shirin daga Adamu Ibrahim Dabo.

Da Dan Gari: Tarihin Garin Janguza, Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:11 0:00


XS
SM
MD
LG