Accessibility links

Da Sanyin Safiya ne Ake ta Jin Harbe-harbe da Tashin Boma-bomai


Mutane sunyi dafifi kewaye da inda boma-boman ya tashi a Maiduguri a ranar 14 ga watan Maris 2014.

Boma-bomai sun tashi da sanyin a birnin Maiduguri a wani hari da yan Boko Haram suka kai.

Tunda sanyi safiyar ne ake ta jin harbe-harbe da kuma tashi boma-bomai a birni Maiduguri, a wani harin da yan boko haram sika kai.

Wanna harin de sun kai shine domin ceto yanuwansu da ake tsare dasu a barikin na sojoji a Maiduguri wadanda aka kama tun chan baya.

Wasu da wakilimu yayi hira dasu ta wayan tarho sun ce sun ga wadansu daga cikin yan boko haram din da aka kubutar sun kudu cikin daji.

XS
SM
MD
LG