Accessibility links

Mutanen Maiduguri Sun Yi ta Bayyana Fargabar da Suka Shiga Ciki Jumma'ar Nan

  • Garba Suleiman

Wasu gidaje da aka kona a harin da ake zaton ‘yan Boko Haram ne suka kaishi a Kawuri dake Maiduguri, Junairu 28, 2014

'Yan bindigar sun kwace dukkan wadanda ake tsare da su a barikin Giwa, amma 'yan Gora da jama'ar gari sun sake damke wasu tare da 'yan bindigar sun mikawa hukuma.

Mutanen garin Maiduguri a Jihar Borno su na ci gaba da bayyana irin taskun da suka shiga jumma'a, a bayan da aka goce da harbe-harbe tare da fashe-fashe da safiyar jumma'ar nan a sassa da dama na birnin, musamman a kewayen barikin Giwa da Jami'ar Maiduguri da kuma wasu unguwannin.

An yi ta barin wuta da luguden bama-bamai har zuwa tsakar rana, yayin da sojojin Najeriya suka yi amfani da jiragen saman yaki wajen kai farmaki a kan 'yan bindigar.

Wasu majiyoyin soja da na fararen hular da suka tattauna da wakilinmu sun ce 'yan bindigar na Boko haram sun samu shiga cikin barikin na Giwa a bayan da aka yi musayar wuta na lokaci, suka kuma saki dukkan wadanda ake tsare da su bisa zargin cewa 'yan Boko Haram ne.

Mutanen gari sun ce sun ga wadannan mutane da aka kubutar su na fadawa cikin daji domin tserewa, amma kuma a wannan karon, ba su ji da dadi ba, domin jiragen sama sun yi ta binsu su na sake musu bama-bamai.

Haka ma fararen hula 'yan banga da ake kira 'Yan Gora ko Civilian JTF sun yi ta bi su na kama 'yan bindigar da kluma 'yan'uwnasu da suka kwato su na mika su ga jami'an tsaro.

Wakilinmu yace mutanen gari sun yi ta kukan kura su na abkawa kan 'yan bindigar, inda suka kama da yawa daga cikinsu, wadanda kwanansu ya kare kuma suka mutu a nan.

Majiyoyin soja sun ce an yi mummunar barna ma 'yan bindigar, wadanda suka iso a fili cikin jerin motoci da babura dauke da bindigogi.

XS
SM
MD
LG