Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kura ta Fara Lafawa a Maiduguri


Jiragen saman yaki na sojojin Najeriya sun fatattaki 'yan Boko Haram da suka kai farmaki kan Maiduguri. An kama 'yan bindiga masu yawa

Rahotanni na baya-bayan nan daga Maiduguri na fadin cewa an fara jin tsit a garin Maiduguri, a bayan kazamin fadan da aka gwabza da safiyar yau har zuwa hantsi a tsakanin 'yan Boko haram da suka kai hari, da sojoji da jama'ar gari da suka maida martani.

'Yan bindigar sun kai farmaki kan barikin Giwa, amma majiyoyi da yawa sun ce ba su samu sukunin shiga ba.

Mazauna unguwannin dake kusa da barikin sun ce sun ga motoci da babura na 'yan Boko Haram sun doshi barikin, amma masu tsaronsa suka ja daga suka bude musu wuta. An yi ta musanyar wuta, kuma daga bisani jiragen saman yaki na sojoji suka kawo dauki, inda suka yi ta cilla bama-bamai kan 'yan bindigar.

Haka kuma, shaidun gani da ido sun fadawa Dandalin VOA cewa sun ga motocin soja da na 'yan Gora, watau Civilian JTF, dauke da 'yan bindigar da aka kama, daure za a tafi da su wani wuri. An gansu sanye da kayan soja, wasu ma da rigunan sulke mai hana harsashi ratsawa.

A kasance da Dandalin VOA domin ci gaba da jin karin bayani na wannan lamarin.
Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG