Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Wahala Japan Ta Iya Gudanar Da Gasar Olympics A Badi


Shugaban Kungiyar aikin jinya ta Kasar Japan ya bayyana cewa zai yi wahala kasar ta iya gudanar da gasar wasannin motsa jiki na Olympic na shekarar badi, ba tare da an samar da allurar rigakafin cutar coronavirus ba.

Yohsitake Yokokura, ya bayyana haka ne a yau Talata, sa'adda yake yiwa manema labari jawabi ta bidiyo a Tokyo babban birnin kasar.

Tun a watan da ya gabata ne Japan da kwamitin wasannin Olympics na duniya su ka amince da a daga gasar ta bana zuwa badi, saboda annobar coronavirus. A da an shirya fara wasanin ne ran 24 ga watan Yuli.

Kamfanonin gwaji da sarrafa magunguna a fadin duniya na ta kara kaimi wajen ganin an samar da maganin cutar, duk da cewa masana na ikirarin cewa zai dau watanni ko shekaru kafin a tabbatar da sahihancin maganin don yin amfani da shi.

Sai dai kuma Yokokura bai fadi ko za’a soke gasar ta badi idan ba’a samar da maganin cutar ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG