Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Hadin Gwiwa A Kasar Iraqi Sun Gano Wani Rami Cike Da Gawarwaki


An gano wani rami cike da gawarwakin wasu mutane da ake tsammanin anyi musu kisan gilla a kusa da birnin Mosul.

Hukumomi a kasar Iraki sun ce dakarun hadin gwiwa dake kai farmaki akan mayakan ISIS kusa da birnin Mosul sun gano wani rami da gawarwakin mutane akalla 100 a ciki kuma duk an dad-datse jikinsu.
Rahotannin da aka samu da farko jiya litinin daga kasashen Yammaci da ‘yan jaridar Kurdawa sun ce ana kyautata zaton gawarwakin fararen hula ne.
Wani mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Iraki ya ce an gano gawarwakin ne a wata kwalejin horas da manoma a wajen garin Hammam al-Alil, kilomita 15 daga kudancin Mosul. Rundunar kuma ta ce an kai kwararrun likitoci wurin don gudanar da binciken kisan gillar da aka yi, da kuma iya tantance mutanen.

Zauren VOA Hausa #EndSARS

Zauren VOA Hausa #EndSARS Kashi na Biyu 03
please wait

No media source currently available

0:00 0:18:31 0:00
Karin bayani akan #ENDSARS: Zanga Zangar Kyamar Gallazawa Al’umma Da Yan Sanda Ke Yi

Rayuwar Birni

Hira da Yusuf, wani dan asalin Jamhuriyar Nijar da ya shekara a Abuja yana sana’r gyaran takalmi
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00
XS
SM
MD
LG