Amma masu sa ido daga kungiyar rajin kare hakkokin jama’a ta Siriyya ta ce har yanzu dai ba a samu wani cigaba ba a farmakin da ake kaiwa.
Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon Peter Cook ya ce “baza mu raina kokarin da za a yi nan gaba ba, yana mai cewa dakarun Siriyya na SDF sun sami nasarori a kwanakin da aka fara kai farmakin, tare da taimakon harin jiragen saman yakin Amurka sabanin abinda ‘yan kungiyar raji suka fadi.
Ma’aikatar Pentagon tayi kokarin rage fargaban da ake yi akan yin hanzarin kai farmaki Raqqa ta kasa, duk da cirjiya da suka fuskanta daga kawayen Amurka, kamar Turkiyya, wadda ta ce kada a kai hari a kan babban birnin ‘yan ISIS dake Siriyya tukuna har sai an gama da tungar mayakan ta karshe dake Mosul, kasar Iraqi.