Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Larabawa Da Na Kurdawa Na Cin Karfin ISIS a Birnin Munjib


Fafatawa a Birnin Manbij

Rahotannin sun nuna cewa, mayakan taron dangi na Larabawa da na Kurdawa na nuna kusan sun kwace ikon wani mawuyacin wuri a arewacin Syria, birnin da yake daya daga cikin manyan wuraren da ‘yan ISIS ke da karfin iko da shi.

Wata kungiyar sa idon ‘yan Syria game da hakkin dan Adam da ke da matsuguni a Birtaniya sun ce, mayakan da ake kira a Turance da Syrian Democratic Forces (SDF) ne suka sake kwace ikon birnin na Manbij.

SDF din dai sun sami mara baya daga dakarun musamman na Amurka ta hanyar ruwan wuta ta sama, bayan sun kaddamar da yakin sake kwato ikon Manjib din daga ISIS.

Wani BaKurde mazaunin Syria Mustafa Bali, kuma mai fafutuka, ya fadawa kamfanin dillancin labaran Associated Press cewa, magana ce ta lokaci, amma dakarun za su kwace ikon Munjib kacokan.

XS
SM
MD
LG