Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun tsaron kasar Siriya sun bude wuta kan 'yan hamayya


Masu zanga zangar kin jinin gwamnati a kasar Siriya
Masu zanga zangar kin jinin gwamnati a kasar Siriya

Dakarun tsaron Syria sun bude wuta kan masu kiraye-kirayen shugaba Bashar al-Assad da yayi murabus. ‘Yan raji da kuam shaidu sun ce an kashe mutane akalla takwas yau Jumma’a a lokacin da dakarun suka dira kan masu adawa da gwamnati.

Dakarun tsaron Syria sun bude wuta kan masu kiraye-kirayen shugaba Bashar al-Assad da yayi murabus. ‘Yan raji da kuam shaidu sun ce an kashe mutane akalla 8 yau Jumma’a a lokacin da dakarun suka dira kan masu adawa da gwamnati. A garin Deir-el-Zour, dake gabashin kasar wanda dakarun gwamnati suka mamaye na tsawon kwanaki, ‘yan gwaggwarmaya da shaidun gani da ido sun ce dakarun sun bude wuta kan masu zanga zanga a akalla kofar masallaci daya a bayan sallar jumma’a. Babu tabbacin ko akwai wadanda suka jikkata. Tun farko yau jumma’a jami’an tsaron kasar Syria sun kai sumame a wurare da dama a saboda fargabar gagarumar zanga zangar da aka shirya yau jumma’a. Masu rajin kare hakin bil’adama da ‘yan gwaggwarmaya sun ce an kashe wata mace bayan da sojoji suka kai farmaki a Khan Sheikhon dake lardin Idlib na arewacin kasar.

An kuma kashe wani mutum bayan da ya nemi gujewa jami’an tsaro a garin Saqba, dake bayan garin Damascus babban birnin kasar Syria. Akalla mutane goma sha shida aka kashe a kasar Syria jiya alhamis yayinda gwamnati ta kara kaimi a yunkunrinta na murkushe ‘yan hamayya, duk da Allah wadai da kasashen duniya keyi da matakan karfi da gwamnatin Bashar al-Assad take dauka a kan masu zanga zanga. Jiya alhamis ne har wa yau sakatariyar ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, a hirarta da tashar talabijin da CBS tayi kira ga kasashen turai da kuma China su kakabawa masana’antun mai da na iskar gas na kasar Syria takunkumi.

XS
SM
MD
LG