Accessibility links

Dalibai a Makarantar Sakandare a Funtua Sunyi Zanga-zanga


Wani aji cike makil da dalibai a Jami’ar Bayero dake Kano, Najeriya. Yuni 11, 2013.

Wasu dalibai dake makarantar Sakandare ta Ideal, sunyi zanga-zanga bayan rashin jin dadin wasu tambayoyi da akayi musu a jarrabawarsu ta fita daga makaranta.

Zanga-zangar ya biyo bayan wasu tambayoyi guda biyu, da suka ce na batanci ne ga Annabi Muhammad S.A.W, wadanda akayi su a tsarin kaci-ci kaci-ci a jarrabawar fita daga makaranta da aka fi kira Mock.

Wakilin Muryar Amurka, Murtala Farouk Sanyinna ya bada rahoton cewa an kona wasu gine-gine a makarantar, amma babu bayani akan rashe-rashen rayuka ko rauni. Shaidun gani da ido sunce sojoji da 'yan sanda sun watsa zanga-zangan ta yin amfani da borkonon tsohuwa, kuma yanzu Kwamishinan 'yan sanda na jihar yana garin na Funtuwa.

Yanzu dai komai ya lafa, kuma zamu cigaba da bincika lamarin. Muna dauke da karin bayani nan ba da jimawa ba.
XS
SM
MD
LG