Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar: An Saki Dalibai Kimanin 100 Da Aka Kama Lokacin Zanga-zanga


Shugaban Nijer Mahamadou Issoufou a wajen Taro kan Tsaro a Najeriya, a Zauren Elysee a Paris, 17 ga, Mayu 2014.
Shugaban Nijer Mahamadou Issoufou a wajen Taro kan Tsaro a Najeriya, a Zauren Elysee a Paris, 17 ga, Mayu 2014.

Hukumomin shari'a a jamhuriyar Nijer Sun sallami wasu dalibai kimanin 100 wadanda jami’an tsaro suka cafke a yayin wata zanga zangar da daliban suka gudanar a ranar 9 ga Watan Afrilu a birnin yamai.

A taron manema labaran da ya kira a wannan alhamis alkali mai shigar da kara da sunan gwamnatin Nijer Procureur de la Republique Chaibou Samna ya sanar cewa an sallami illahirin daliban da aka kama saboda zarginsu da hannu a fashe fashen da kone konen da aka yi a yayin wata zanga zangar daliban makarantun secondary ta ranar 9 ga watan Afrilu anan Yamai. Tuni dai iyayen yaran da abin ya shafa suka biya kudaden da suka yi dai dai da darajar dukiyoyin da aka bannata.

A karshen makon jiya ne alkali mai shigar da kara da sunan gwamnatin nijer Procureur de la Republique Chaibou Samna ya bukaci mutanen dake korafin an yi masu barna a yayin zanga zangar dalibai ta ranar 9 ga watan afrilun 2019 su yi rajista a ofishin hukumar ‘yan sandan domin duba hanyoyin biyan kudaden dukiyoyin da aka bannata masu lamarin da ya bada damar tuntubar mahaifan yaran da abin ya shafa.

Ma’aikatar magajin garin yamai na daga cikin wadanda ke korafin an yi masu barna a yayin wannan zanga zanga.

Sai dai kungiyar daliban makaratun secondaryn Yamai a ta bakin sakatarenta Adibis Alio na mai nun arashin gamsuwa da wannan mataki.

Hukumomin shara’ar Nijer na ganin matakin a matsayin wata hanyar ladabtarwa kokuma jan kunne ga matasan wannan kasa ta yadda zasu bambanta ‘yanci da hakkin dan kasa.

Matakin soke tsarin bayar da karatun bayan fage da wasu malamai kan baiwa dalibai da sharadin biyan kudade da ake kira cours d’appui ne mafarin zanga zangar ta ranar 9 ga watan afrilu. A yayin da daliban ke ganin tsarin na taimaka masu wajen cike gibin karatu ita kuwa gwamnati cewa take akwai yaudara tattare da wannan tsari saboda ba rabon ‘yayan talakkawa a cikinsa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG