Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalibi Na 3 Ya Mutu Daga Cikin Wadanda Aka Harba A Ohio


Wata dalibar makarantar sakandaren Chardon na aza furannin karrama wadanda harin ya rutsa da su
Wata dalibar makarantar sakandaren Chardon na aza furannin karrama wadanda harin ya rutsa da su

Russell King mai shekaru 17 ya mutu talatar nan sanadiyar harbin sa da aka yi

Hukumomi sun ce dalibi na uku ya mutu sanadiyar harbin mai kan uwa da wabin da ya faru jiya Litinin a jahar Ohio, da ke yankin tsakiyar Amurka.

Shugaban ‘yan sandan birnin Chardon ya ce da jijjifin talatar nan Russell King mai shekaru 17 ya yi sallama da duniya. A jiya Litinin wani dalibi ya bude wuta kan sauran dalibai a dakin cin abincin makarantar sakandare ta Chardon. A jiya Litinin din jim kadan bayan harbin dalibi daya dan shekaru 16 ya ce ga garin ku, yanzu dalibai uku sun mutu, wasu biyu na kwance a asibiti.

Hukumomi sun ce jiya litinin da marece sun kama wani matashin da ake zargi da aikata harbin. Shaidu da kafofin yada labaran birnin sun ce yaron da aka kama sunan shi T.J.Lane, kuma dalibi ne a wata makarantar kangararrun yara da ke kusa da makarantar da ya je ya yi harbin.

T.J.Lane ya yi bayyanar shi ta farko a gaban kotu Talatar nan. Hukumomi sun ce har yanzu babu tabbas game da dalilin kai harin.

Da yammacin jiya Litinin wani lauyan Lane ya shaidawa manema labaran birnin cewa iyayen shi na cikin matukar tashin hankali kuma su na so su mika ta’aziyar su ga iyayen yaran da harbin ya rutsa da su. Lauyan ya ce wanda ake zargin shuru-shuru ne, kuma yaron kirki ne wanda, shi dai a sanin shi, bai taba shiga wata rigima ba.

A daidai lokacin da hukumomi ke ci gaba da gudanar da bincike akan harbin, Talatar nan ma an rufe makarantu a garin Chardon mai mutane kimanin dubu biyar.

XS
SM
MD
LG