Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Guguwa Ta Yi Barna Mai Yawa A Amurka


Mutane akalla 27 suka mutu jumma'a a a wasu jihohi uku, a bayan 13 da irin wannan guguwa ta kashe ranar laraba a wasu jihohin dabam

Guguwa mai tsananin karfi ta kashe mutane akalla 27 a jihohi da dama dake nan gabashin Amurka, ta kuma haddasa hasarar dukiyar da wasu sassan ba su taba ganin irinta ba.

Hukumomi sun ce guguwar ta jiya jumma’a ta kashe mutane 12 a Jihar kentucky, da 13 a Jihar Indiana da kuma 2 a Jihar Ohio.

Irin wannan guguwa mai tsanani da ake kira Tornado ko kuma Twister, ta shafe wani gari mai suna Henryville a Jihar Indiana. Guguwar ta rgargaza motoci ta dauki wata motar bas ta ‘yan makaranta sama ta jefa ta kan wani gida da wurin saida abinci.

Jami’ai a garin Marysville a Jihar Indiana, sun ce babu gida ko guda daya da ya rage a garin nasu.

An kuma bayarda rahoton barna mai dan karen yawa a kusa da birnin Louisville a Jihar kentucky, inda hancin wata guguwar ya sauko kasa yayi barna jiya jumma’a da maraice.

Irin wannan yanayi mai tsanani ya zo ne kwanaki biyu kacal bayan barkewar mummunar guguwa ta farko a wannan shekarar, inda mutane 13 suka hallaka a yankunan tsakiya da kuma kudu a nan Amurka.

Gagarumin hadarin ruwan saman da ya janyo wannan guguwa ya keta ta jihohin Illinois da Missouri da kuma Tennessee ranar laraba, ya kuma haddasa guguwa mai tsanani a jihohin Kansas da Kentucky.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG