Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Aka Yi Karin Kudaden Aikace-Aikace a Asibiti


Wasu marasa lafiya da ke kwance a asibiti
Wasu marasa lafiya da ke kwance a asibiti

Hukumomin kula da Asibitin koyarwa na Aminu Kano, sun yi karin haske dangane da dalilan karin kashi dari bisa dari na kudaden aikace-aikace ga marasa lafiyar dake ziyartar asibitin.

Kimanin makonni biyu da suka gabata ne mahukuntan sibitin suka sanar da Karin kudaden da marasa lafiya ke biya domin ganin likita da sauran aikace –aikacen kiwon lafiya. Karin kashi dari ne dai hukumomin suka yi akan dukkanin aikace-akaice da suke yi.

Sai dai masu nazari akan tsarin kiwon lafiyar Jama’a sun kawo shawarar hanyoyin bi domin magance matsalolin dake haifar tsadar kiwon lafiya a kasashe irin su Najeriya.

Al’uma, musamman marasa lafiyar dake ziyartar asibitin sun koka da wannan kari, la’akari da tsadar rayuwar da ake ciki.

Sai dai Farfesa Auwalu Umar Gajida mataimakin shugaban asibitin ya fayyace dalilan daukar wannan mataki. Ya ce saboda canje-canje kayayyakin aiki musamman irin su gas ne ya sa dole sai sun chanza farashin su.

Yanzu haka dai masana kiwon lafiya da masu sharhi kan harkokin lafiya a Najeriya na bada shawarwari kan matakan da ya kamata a dauka a irin wannan yanayi.

Dr Musa Sufi guda cikin masu tsokaci a fagen kiwon lafiya a Najeriya na cewa ya kamata gwamnatoci su fito da tsari na tallafi na gaggawa don rage wa al'umma, don kawo masu sauki.

Sai dai wannan karin da mahukuntan na Aminu Kano su ka yi na wucin gadi ne, inji Farfesa Auwalu Umar Gajida.

Mai gadajen kwanciya kimanin 700, a shekara ta 2017, fiye da mutane dubu dari uku ne suka ziyarci wannan asibitin koyarwa na Aminu Kano dake birnin Kano.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

XS
SM
MD
LG