Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lionel Messi Ya Bar Barcelona 


Messi a shekarar 2019 lokacin suna shirin karawa da Atletico Madrid
Messi a shekarar 2019 lokacin suna shirin karawa da Atletico Madrid

“FC Barcelona na mika godiyarta ga dan wasan bisa irin rawar da ya taka wajen dabbaka kungiyar, tana kuma masa fatan alheri a duk in da zai je.”

Kungiyar Barcelona FC ta kasar Sifaniya ta ce dan wasanta Lionel Messi ya bar kungiyar.

Barcelona ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter a ranar Alhamis inda ta ce lamarin na da nasaba da batun kudade da kuma wasu al’amura da suka shafi ka’idojin gasar La Liga.

“Duk da cewa FC Barcelona da Lionel Messi sun cimma matsayar rattaba hannun kan sabon kwantiragi a yau, hakan ba zai yi wu ba, saboda matsaloli na kudi da wasu al’amura.” In ji Barcelona.

Kungiyar ta kara da cewa, a dalilin hakan, dan wasan wanda dan asalin Argentina ne ba zai zauna a kungiyar ba.

“Dukkanmu mun yi takaicin cewa, burin kungiyar da na dan wasan ba su cika ba.”

“FC Barcelona na mika godiyarta ga dan wasan bisa irin rawar da ya taka wajen dabbaka kungiyar, tana kuma masa fatan alheri a duk in da zai je.”

A watan da ya gabata, Messi ya amince ya sabunta kwantiraginsa zuwa tsawon shekara biyar inda aka rage kudaden da za a rika biyansa.

Euro miliyan 500 Barcelona ta biya Messi kan kwantiragin shekara hudu, wanda ya kare a ranar daya ga watan Yuli.

Messi dan shekara 34, ya kwashe daukacin rayuwarsa ta kwallo ne a kungiyar ta Barcelona.

Ko da yake, ya yi yunkurin barin kungiyar a kakar wasa ta shekarar 2019-20, bayan da ya nuna cewa ba ya jin dadin inda kungiyar ta dosa.

A baya, akwai manyan kungiyoyi da suka nuna sha’awar sayen dan wasan, amma rahotanni na cewa wakilansa da hukumomin kungiyar ta Barcelona suna kan tattaunawa kan wani sabon kwantiragi.

Yunkurin komawar Messi PSG Ya Hadu Da Cikas

Lionel Messi: Yunkurin komawar Messi PSG Ya Hadu Da Cikas
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:21 0:00

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG