Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Shan Kayen Liverpool Zai Yi wa Manchester City Dadi


Wasan Liverpool da Leicester City inda aka doke Liverpool da ci 1-0
Wasan Liverpool da Leicester City inda aka doke Liverpool da ci 1-0

Gabanin kwallon da Lookman ya zura a ragar Liverpool, Mohamed Salah ya zubar da bugun fenariti a minti na 16.

Liverpool ta sha kaye a hannun Leicester a wani yanayi na ba-zata a gasar Premier League ta Ingila.

Leicester ta doke Liverpool da ci 1-0 a wasan wanda aka kara a daren Talata.

Dan wasan Leicester Ademola Lookman ne ya zura kwallo a ragar Liverpool a minti na 59.

Gabanin kwallon Lookman, Mohamed Salah ya zubarwa da Liverpool bugun fenariti a minti na 16.

Wannan shi ne karo na biyu da kungiyar ke shan kaye a wannan kakar wasa, lamarin da ya sa Manchester City da ke jagorancin teburin gasar ta ba Liverpool tazarar maki shida bayan wasanni 19.

Shi ma Sadio Mane ya zubar da wata babbar dama a minti na 55, minti hudu kafin Lookman ya zura kwallonsa.

Ita dai Manchester City za ta kara da Brentford a ranar Laraba, wanda akwai yiwuwar ta lashe wasan.

Liverpool da ke biye da ita a baya a teburin gasar za ta kara da Chelsea a ranar 2 ga watan Janairu.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG