Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Damokaradiyya Ake a Najeriya Ko kuwa Mulkin Farar Hulla

Wasu matasa 'yan bangar siyasa
Wasu matasa 'yan bangar siyasa

A bangaren siyyasa kuma a wannan makon, Wasu matasa naganin yakamata ayiwa tukkan hanci. A cewar Mal. Anas Saminu Ja'in Makera, yace lallai a Najeriya, ba damokaradiyya a keyi ba ana dai mulkin farar hullane kawai, don idan a na mulkin damokradiyya to lallai za'a mutunta wasu shariddodi na damokradiyya guda hudu. Na farko a cewar Mal. Anas, shine 'yansiyasa su dinga duba cancanta wajen tsayar da 'yantakara na gari, na biyu a tabbatar da anyi zabe na gari akan lokaci, da kuma kauce ma magudi, kana na uku a dinga yin biyayya ga kundin tsarin mulkin kasar, sai abu na hudu me matukar mahimanci shine bin doka da oda.

Yace dai a nashi ganin 'yansiyasa sun barranta da duk wadannan tsarurukan, ganin cewar an daura matasa bisa ga wani sashi na yaza'ayi ai amfani dasu wajen bangar siyasa ga 'yan hamayya, yace wannan ba tsari bane na damokaradiyya. Yayi kira ga matasa da su hankalta su yi karatun ta natsu kada su bari ayi amfani da su wajen cinma wani buri wanda daga bisani za'a yar dasu.

Shi kuma Mal. Balarabe, yace lallai maganar Mal. Anas, tana kan hanya, sannan kuma yakamata asani cewar su wadannan matasan sun kasu kashi daban daban, ganin yadda akasamu kai yanzu cikin wani sabon tsari na yanar gizo wanda ake aikawa da wasu sakonni don tada zaune tsaye, don haka al'umma su gane sukuma yi hankali.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG