'Yan siyasa na kara kira ga al'ummomi da su kaurace ma bangar siyasa, ganin yadda zabe ke kara karatowa a wannan kasa ta Najeriya. A cewar wani me neman takarar kujerar majalisar wakilai Alh. Abdullahi A. Ibrahim a jihar Taraba, yace yakamata matasa da sauran al'umma suyi karatun ta natsu, da kuma kada subari ayi amfani da su wajen tada zaune tsaye. Yakamata a yi siyasa ba da gababa, kamar yadda akecewa.
Ya bukaci kuma 'yan siyasa da su maida hankali wajen gudanar da yakin nemanzabe bisa ga kwanciyar hankali da lumana, kuma su guji yin amfani da 'yayan wasu kasancewar babu wanda zai yi amfani da nashi yara wajen bangar siyasa.
Tabaki Sanata Hajia Aisha Alhasan, 'yar takarar shugabancin gwamna a jihar Taraba a karkashin jam'iyar adawa ta APC, tana zargi cewar rashin shugabanci nagari shike kawo matsalolin da ake fuskanta a kasar baki daya, tana ganin cewar matasa na gama karatu amma babu aikin yi, ta kara da cewar ba dole ne kowane yaro yaje jami'a ba saboda kowane yaro da irin baiwar da Allah yayi masa, don haka kada kowa yace ba zai nemin na kanshi ba don dogaro da neman zama wani abu a rayuwa. Ta kuma yinuni da cewar an cucesu a jihar Taraba ganin yadda gwamnati batayi musu komai ba, baya ga irin arzikin kasa da Allah yayi musu a jihar, tace don haka yakamata mutane su riki noma da sauran sana'o'i.